Kamfanin dillancin labaran dpa ya ce Dareen Wilson dan shekara 28 a duniya yay i ritaya ne bayan da yaga sauran abokan aikinsa suna cikin tsaka mai wuya sanadiyyar tashe tashen hankula da suka bazu a birana ne da daman a kasar.
A ranar 9 ga watan Augustan da ta gabata ce Wilson ya harbe Michel Brown dan shekara 18 bakar fata Missouri na kasar Amurka , hakan ya jawo tashe tashen hankula a kasar, wanda ya kuma tilastawa hukumomi gurfanar da shi a kutu. Sai dai kotun ta wanke shi bayan wani lokaci don abinda ta kira rashin wata hujja na hukunta shi. Hukuncin dai ya sake ruruta wutan rikici a kasar inda bakaken fatan Amurka suke ganin jami'an tsaro fararen fatar kasar basa masu adalci.abna